Wasanni-Kwallon kafa

Kungiyar Bayern zata kara da PSG a wasan karshe

Gasar cin kofin zakarun Turai a Lisbon na kasar Fotugal
Gasar cin kofin zakarun Turai a Lisbon na kasar Fotugal REUTERS/Eric Gaillard

Yau lahadi kungiyar Bayern Munich zata kara da Paris Saint Germain a wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar Turai da zai gudana a birnin Lisbon na kasar Fotugal.Kungiyar Bayern Munich ta lashe wannan kofi har sau 5, yayin da PSG bata taba samun nasarar lashe shi ba.

Talla

Kungiyar Munich na gadara da fitattun Yan wasan ta irin su Robert Lewandowski da ake yiwa lakabi da ‘dodan raga’ da Muller da Alaba da

Ita kuwa PSG tana tinkaho ne da matasan Yan wasa irin su Neymer da Kylian Mbappe da Angel Di Maria da Icadi wadanda suka taka gagarumar rawa wajen ganin kungiyar ta samu nasarar zuwa wannan matsayi.

Yaya kuke ganin wannan wasa zai kaya?

Muna dakon ra’ayoyin ku

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.