Tinubu ya Tarawa Buhari kudin kamfe - Babacir
Tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya Babacir Lawal yace Bola Ahmed Tinubu ne ya taka gagarumar rawa wajen tarawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kudin yakin neman zaben da ya taimaka masa samun nasarar zaben shekarar 2015.
Wallafawa ranar:
A wata hirar da yayi da Jaridar Punch, Babacir yace Buhari da magoya bayan sa basu da kudin da zasu iya taimaka masa lashe zabe, sai dai manufofi da kuma goyan bayan da suke da ita a hannun wasu Yan Najeriya.
Tsohon Sakataren Gwamnatin yace Tinubu yayi amfani da Yan kasuwar da ya sani wajen tara makudan kudaden da Buhari yayi amfani da su wajen kayar da shugaba Goodluck Jonathan a zaben da akayi.
Babacir yace daga cikin wadanda suka bada gudummawa harda wasu dake kusa da gwamnatin Jonathan saboda yadda suka gamsu da tabbacin da Tinubu ya gabatar musu.
Tsohon Sakataren Gwamnatin yace shi da ministan man fetur Timipre Sylva sun yi iya bakin kokarin su wajen ganin sun samawa Buhari kudaden yakin neman zabe amma sai suka gaza, har sanda Tinubu ya sanya hannu.
Babacir yace bayan kudaden tallafi da Tinubu ya samawa Buhari, yayi kuma amfani da dukiyar sa wajen yakin neman zaben da kuma dauko hayar wadanda suka taimakawa tsohon shugaban Amurka Barack Obama yakin neman zabe wajen tallata shugaba Muhammadu Buhari.
Tsohon Sakataren yace shigowar wadancan mutane daga Amurka ya sa Buhari ya fara bayyana da kayan Yarbawa da Igbo da Kanuri, kana ya fara bayyana a hotuna tare da iyalan sa.
Babacir yace a lokacin ne kuma aka fara fito da uwargidan sa Aisha Buhari tana halartar tarurruka da kuma jawabi domin nema masa goyan baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu