Jamhuriyar Congo

'Yan ta'adda sun halaka mutane 13 a Jamhuriyar Congo

Wasu dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya, yayin aikin sintiri a garin Djugu dake lardin Ituri, a gabashin Jamhuriyar Congo. 13/3/2020.
Wasu dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya, yayin aikin sintiri a garin Djugu dake lardin Ituri, a gabashin Jamhuriyar Congo. 13/3/2020. © Samir Tounsi / AFP

Rahotanni daga Jamhuriyar Congo sun ce mayaka masu ikirarin Jihadi na kungiyar ADF sun halaka mutane 13, yayin farmakin da suka kaiwa wasu kauyuka biyu dake gabashin kasar ta Congo.

Talla

Bayanai sun ce mayakan na ADF sun yiwa fararen hular kisan gilla ne bayan daurin da suka musu, a kauyukan Kinziki-Matiba da kuma Wikeno.

Tuni dai majalisar dinkin duniya tayi tur da kashe-kashen, tare da bayyana shi a matsayin laifin yaki,

Kididdigar da majalisar ta fitar a baya bayan nan ta nuna cewar mayakan na ADF da cibiyarsu ke Uganda sun halaka akalla mutane dubu 1 daga farkon shekarar 2019 zuwa yanzu, mafi akasari a lardin Kivu dake Jamhuriyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.