Najeriya:IPOB sun kashe mana jami'ai biyu - DSS

Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB.
Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB. REUTERS/Afolabi Sotunde/Files

Rundunar Tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta ce masu fafutukar kafa kasar Biafra sun kashe jami’an su guda 2 a arangamar da suka yi a Jihar Enugu, yayin da kungiyar ta ce jami’an tsaron sun kashe mata mutane 21.

Talla

Kakakin rundunar DSS Peter Afunanya ya ce 'yan kungiyar IPOB sun kaiwa motar jami’an su hari a Emene dake Enugu, inda aka hallaka biyu, kuma yanzu haka suna farautar wadanda ke da hannu wajen aikata kisan.

Ita ma kungiyar IPOB ta bakin kakakinta Emma Powerful ta zargi jami’an tsaron Najeriya da kashe mata ‘yaya 21, inda yake cewa kungiyar su ta zaman lafiya ce.

Sanarwar ta DSS ba ta ce an kashe wani dan kungiyar awaren Biafra ba, haka kuma babu wata hanyar tabbatar da cewa an kashe mutane har 21.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam a ciki da wajen kasar sun sha zargin jami’an tsaron Najeriya da kisan ‘yan kungiyar IPOB.

A shekarar 2016, kungiyar kare hakkin dan adam ta  Amnesty International ta zargi jami’an tsaron Najeriya da yi wa wasu mambobin kungiyar IPOB 150 kisan gilla, zargin da hukumomin kasar suka musanta.

Kungiyar IPOB da ke neman a ware mata ‘yantatar kasar al’ummar Ibo daga Najeriya ta sha yin arangama da hukumomin tsaron kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.