Bakonmu a Yau

Najeriya:Kabilun da ke rikici a Zangon Kataf sun yi sulhu

Sauti 03:33
Taswirar Najeriya da ke nuna yankin  kudancin Kaduna.
Taswirar Najeriya da ke nuna yankin kudancin Kaduna. Premium Times Nigeria

Kabilun Atyap da Fulani da Hausawa dake rikici a Zangon Kataf dake Jihar Kaduna a  Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin su.Wannan ya biyo bayan taron zaman lafiyar da Basaraken yankin, Agwatyap, Dominic Gambo Yahya ya jagoranta tare da tsohon hafsan sojin sama mai ritaya, Air Marshall Stephen Shekari da kuma wakilan al’ummomin 3 dake yankin.Dangane da wannan nasarar da aka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barista Francis Kozah daya daga cikin mahalarta taron, kuma ga yadda tattaunawar ta kaya.