Mali-Afrika

Sojin Mali za su mika mulki cikin shekaru 3

Ibrahim Boubacar Keita, hambararren shugaban kasar Mali.
Ibrahim Boubacar Keita, hambararren shugaban kasar Mali. RFI-France 24

Sojojin da suka yi juyin mulki a Mali sun bayyana aniyar su ta gudanar da gwamnatin rikon kwarya na shekaru 3 wanda zai kaiga gudanar da sabon zabe, yayin da suka amince su saki tsohon shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita.

Talla

Majiya daga tawagar kungiyar ECOWAS da ta gana da su a Bamako ta ce sojojin sun bukaci kafa majalisar mulki ta soji  domin jagorancin gwamnatin, a daidai lokacin da suke cewa basu damu ba idan tsohon shugaban kasar Keita na bukatar barin Mali domin kula da lafiyar sa.

Wani jamia’in gwamnatin sojin na Mali ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Faransa cewa za su tafiyar da kasar na tsawon shekaru 3 da gwamnatin da zai kunshi akasari hafsoshin jami'an soji.

Jami’in ya kara da cewa sojojin sun amince su saki hambararren shugaba Boubacar Keita da suka tsare tare da sauran ‘yan siyasa, kuma har zai koma gida cikin iyalansa ko kuma ya bar kasar don duba lafiyarsa idan yana so.

Za a kai firaminista Boubou Cisse, wanda tare da Keita aka kama su wani kebantaccn  wuri a babban birnin kasar.

Yayin da ake ta sukar wannan juyin mulki daga wajen kasar, dubban masu goyon bayan ‘yan adawa sun fito ne suna murnar hambarar da shugaba Keita a titunan babban birnin kasar Bamako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.