Afrika-Polio

Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar da kawo karshen polio a Afrika

Jami'ai yayin bada allurar rigakafin cutar polio a Najeriya
Jami'ai yayin bada allurar rigakafin cutar polio a Najeriya PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar a hukumance cewar nahiyar Afirka ta rabu da cutar polio bayan kwashe shekaru da dama ana yaki da ita wajen bada allurar rigakafi a kasashen duniya da dama.

Talla

Farfesa Rose Gana Fomban Leke da ta jagoranci binciken da ya tabbatar da babu wanda ke dauke da cutar ta sanar da matakin, inda ta bayyana yau a matsayin rana mai dimbin tarihi ga Afirka.

Da wannan mataki Afirka tayi nasarar kawar da cutar polio daga nahiyar kamar yadda aka yiwa cutar kyanda.

Tun daga shekarar 1996 Hukumar Lafiya ta fara yaki da cutar polio wajen yiwa yara rigakafi abinda ya kaiga kare yara miliyan guda da dubu 800 daga zama guragu da kuma kare rayukan mutane 180,000.

A shekarar 1988 da Hukumar Lafiya da Hukumar UNICEF da Rotary suka kaddamar da yaki da cutar, duniya na dauke da masu dauke da cutar 350,000, yayin da sama da 70,000 ke nahiyar Afirka.

Hukumar ta ce a cikin shekaru 30 da suka gabata, an kashe akalla Dala biliyan 19 wajen yaki da cutar, yayin da yanzu banda kasashen Afghanistan da Pakistan babu wata kasa dake dauke da cutar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla ma’aikata sama da 20 suka rasa rayukan su wajen aikin yaki da cutar, saboda haka wannan gagarumar nasara ce aka samu wajen ganin bayan ta a Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.