Jagoran 'yan adawan Kamaru ya yi barazanar kifar da gwamnatin shugaba Biya
Jagoran ‘yan adawa a Kamaru Maurice Kamto, ya yi barazanar shirya zanga-zangar da za ta kawo karshen mulkin shugaba Paul Biya, matukar dai shugaban ya ce zai shirya zaben larduna ba tare da an cika wasu sharudda ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kamto, dan takarar jam’iyyar MCR a zaben shugabancin kasar da aka yi cikin 2018, a taron manema labarai da ya jagoranta a birnin Yaounde, ya ce dole ne a cika wadansu sharuda, da suka hada da samar da zaman lafiya da ‘yan aware, sannan a bude tattaunawa tsakanin gwmanati da sauran jam’iyyun siyasar kasar, idan ba haka ba kuwa zai jagoranci zanga-zangar da za ta kawo karshen mulkin shugaba Paul Biya.
A wannan karo dai Kamto, wanda ya zo na biyu ta fannin yawan kuri’a a zaben da ya gabata, ya ce ba ya da niyyar kaurace wa zaben lardunan kasar da za a yi nan ba da jimawa ba kamar yadda ya yi a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da aka yi cikin watan fabarairun da ya gabata.
A maimakon haka jagoran ‘yan adawar ya ce ba ta yadda za a shirya wani zabe a yanayin da kasar ta ke ciki a yau, kuma yunkurin shirya wani zabe zai kasance dalilin kawo karshen mukin shugaba Biya, kuma za a kawar da shugaban ne ta hanyar shirya tarzoma a kan titunan kasar a cewarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu