Bakonmu a Yau

MDD ta bukaci Buhari ya yi amfani da tattaunawa wajen shawo kan matsalar tsaro a Najeriya

Sauti 03:37
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria Presidency/Handout via REUTERS

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da yayi amfani da tattaunawa da kuma tafarkin siyasa wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar.Babban Jakadan Majalisar dake Najeriya Edward Kallon ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa fadar shugaban, inda yake cewa matsalolin tsaron da suka addabi kasar dake da sassa daban daban na da wahalar magance su.Dangane da wannan shawara Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Ibrahim Kazaure, tsohon ministan ayyuka na musamman a Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.