Najeriya: Zulum ya gana da al’ummar Magumeri bayan harin ta’addanci

Gwamnan jihar Borno a Najeriya Babagana Umara Zulum ya ziyarci garin Magumeri a Talatar nan bayan harin da kungiyar Boko Haram ta kai yankin.

Gwamnan jihar Borno a Najeriya yayin ziyarar da ya kai Magumeri bayan harin Boko Haram.
Gwamnan jihar Borno a Najeriya yayin ziyarar da ya kai Magumeri bayan harin Boko Haram. RFI Hausa
Talla

Gwamnan ya yi jawabi ga al’ummar garin, kana ya duba irin ta’adin da harin Boko Haram ya yi a kan babban asibitin Magumerin.

A jawabin nasa, ya bukaci al’ummar da su kai rahoton duk wani abin da suke zargin yana barzana ga zaman lafiyar yankinsu, yana mai bayyana mahimmancin sanar da hukuma abubuwan da k iya zama tarnaki ga zaman lafiya.

Zulum ya umurci ma’aikatar sake gina jihar da su hada kai da ma’aikatar lafiya wajen sake gina asibitin da harin ya barnata da ma kayayyakin aiki da ke cikinsa.

Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na fama da hare hare daga kungiyar Boko Haram fiye da shekaru 10 kenan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI