Amurka-Sudan

Pompeo na ziyarar farko a Sudan don gyara alakar kasar da Isra'ila

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo. Andrew Harnik/Pool via REUTERS

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya isa Sudan yau Talata, a ziyara irinta ta farko da wani jami’in Diflomasiyya daga Amurkan ke kai wa Sudan cikin shekaru 15 da suka gabata.

Talla

Ziyarar ta Pompeo wani bangare ne na neman goyon bayan kasashen Larabawa da Amurka ke yi tun bayan sabuwar alakar diflomasiyya tsakanin Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Pompeo, wanda kai tsaye jirginsa ya taso daga Tel Aviv zuwa Sudan ita ce ziyara irinta ta farko tun bayan 2005 da wani jami’in Amurka ke kaiwa kasar, inda kai tsaye zai gana da Firaminista Abdallah Hamdok kana shugaban majalisar gwamnatin hadaka Janar Abdel Fattah al Burhan.

Tsawon shekaru dai Sudan na fuskantar takunsaka da Amurka baya ga rikici da Isra’ila karkashin jagorancin tsohon shugabanta Omar al-Bashir da ke goyon bayan masu tsattsauran ra’ayi, sai dai sabuwar gwamnatin hadakar kasar ta sha alwashin gyatta alakokin da suka samu nakasu karkashin jagorancin tsohon shugaban.

Sudan, dai na da fatan samun sassauci daga matsin lamba da takunkuman Amurka baya ga cireta daga jerin kasashe masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci bayan samar da sauye-sauye a salon shugabanci da tafiyar da harkokinta.

A bangare guda Sudan na kallon kyautata alaka tsakaninta da Isra’ila tsohuwar abokiyar gabarta kuma shalelan Amurka zai taimaka wajen samun fadaa a wajen Amurkan, dalilin da ya sanya alkawarta kulla sabuwar alaka tsakanin kasashen biyu yayin ganawar Benjamin Netanyahu da Burhan a Uganda, wanda kuma ziyarar Pompeo ke shirin jadadda alakar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.