Afrika-Polio

WHO za ta sanar da kawo karshen Polio a Afrika baki daya

Najeriya na daya daga cikin kasashen da cutar ta dade a Afirka.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da cutar ta dade a Afirka. AFP/Getty/PIUS UTOMI EKPEI

Yau ake saran Hukumar Lafiya ta Duniya WHO za ta bayyana kawo karshen cutar polio a nahiyar Afirka, shekaru 4 bayan samun wanda ya ke dauke da cutar guda a arewa maso gabashin Najeriya.

Talla

Sanarwar da Hukumar lafiyar ta gabatar, ta jinjinawa gwamnatocin Afirka da masu bada agaji da jami’an kiwon lafiya da al’ummomin da suka bada gudumawa wajen ceto yara akalla miliyan guda da dubu 800 daga zama guragu sakamakon cutar.

Da misalin karfe 3 agogon GMT ake saran shugaban Hukumar Lafiya Tedros Adhanom Gebreyesus da wasu fitattun mutane cikin su harda Bill Gates za su gabatar da rahotan wanke nahiyar.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da cutar ta dade a Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.