Mali-ECOWAS

ECOWAS da Sojin Mali sun gaza cimma matsaya kan mika mulki ga farar hula

Wakilan kungiyar ECOWAS a ganawarsu da jagorancin Sojin da suka yi juyin mulki a Mali.
Wakilan kungiyar ECOWAS a ganawarsu da jagorancin Sojin da suka yi juyin mulki a Mali. REUTERS/Mamadou Keita

Tattaunawa tsakanin Jakadun kungiyar ECOWAS da sojojin da suka yi juyin mulki a Mali ta karkare ba tare da amicewa da shirin mayar da mulki ga fararen hula tsakanin bangarorin biyu ba.

Talla

Bangarorin biyu duk sun bayyana matsayin tsohon shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita cewar baya bukatar komawa karagar mulki, amma kuma bukatar sojojin na mulkin shekaru 3 kafin gudanar da zabe bai samu amincewar tawagar ta ECOWAS ba.

Ana saran tawagar a karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ta gabatar da rahoto ga shugabannin kasashen da ke yankin.

Mali ta fada rikicin siyasar da ya kai ga boren al'umma tare da juyin mulki ne tun bayan zaben shiyyoyi da jam'iyya mai mulki ta tsohon shugaba Boubacar Keita ta samu rinjaye.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.