Mali-ECOWAS

ECOWAS ta bukaci sojin Mali ta mika mulki bayan shekara guda

Shugaban ECOWAS, kuma shugaban Mahamadou Issoufou yaayin da ya isa Bamako babban birnin Mali, 23 ga watan Yuli,2020.
Shugaban ECOWAS, kuma shugaban Mahamadou Issoufou yaayin da ya isa Bamako babban birnin Mali, 23 ga watan Yuli,2020. MICHELE CATTANI / AFP

Jakadun Kungiyar ECOWAS wajen sasanta rikicin Mali sun yiwa sojojin da suka yi juyin mulki a kasar tayin gudanar da mulkin shekara guda wanda zai basu damar gudanar da zaben da zai mayar da mulki a hannun farar hula.

Talla

Fadar shugaban Najeriya ce ta sanar da haka, inda take cewa watanni 12 zasu baiwa gwamnatin rikon kwaryar damar shirya karbabben zaben da zai dora fararen hula a mulki.

Wannan na daga cikin abinda shugaban tawagar Goodluck Jonathan ya shaida wa shugaba Muhammadu Buhari lokacin da yayi masa bayani kan ziyarar da suka kai Mali da kuma tattaunawar da suka yi da bangarorin dake rikici a  kasar.

Rahotanni sun ce sojojin da suka yi juyin mulkin sun ki amincewa da bukatar mika mulki cikin shekara guda, inda suka ce suna bukatar shekaru 3 domin tabbatar da cewar al’amura sun koma daidai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.