Najeriya

Miliyoyin Hausawa na gudanar da bikin ranar Hausa ta Duniya

Wasu makadan Hausawa.
Wasu makadan Hausawa. Reuters

Miliyoyin Hausawa ne ke bikin ranar Hausa ta duniya da ke gudana kowacce ranar 26 ga watan Agusta a ilahirin yankunan Hausawa da sauran sassan duniya da Hausawan ke rayuwa.

Talla

Ranar wadda yau ne karo na 6 da ake gudanar da bikinta na da nufin hada kan Hausawa baya ga samar da ci gaba mai dorewa dama bunkasa harshen, wanda ke matsayin na biyu mafi girma a nahiyar Afrika.

Harshen na Hausa wanda kusan galibin kasashen yammacin Afrika ke amfani da shi da kaso mai yawa a Najeriya, na daga cikin yare mai saurin yaduwa a nahiyar Afrika dama wasu sassa na duniya ta yadda harshen ke yin awon gaba da kananun yarukan da ke makwabtaka da Hausawa.

Kawo yanzu dai babu sahihin bayani kan asali ko kuma lokacin da aka fara amfani da harshen Hausa a ban kasa, amma batutuwa da dama na alakanta saurin yaduwarsa da fataucin da aka san Bahaushe da yi zuwa sassan duniya, kafin daga bisani kafofin yada labarai su sake bunkasa harshen.

Baya ga harshen Swahili da ke da alaka da larabaci Hausa ce kan gaba a jerin harusunan da ake amfani da su a nahiyar Afrika dama yawan jama’ar da ke amfani da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.