Sudan ta ki yadda da sabunta alaka da Isra'ila

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da Firaministan Sudan Abdalla Hamdok yayin ganawarsu a Khartoum.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da Firaministan Sudan Abdalla Hamdok yayin ganawarsu a Khartoum. Handout / Office of Sudan's Prime Minister / AFP

Gwamnatin rikon kwarya a Sudan, ta ce ba ta da hurumin sake dawo da huldar diflomasiyya tsakanin kasar da Isra’ila, saboda wannan ba ya daga cikin ayyukan da suka rataya a wuyanta.

Talla

Firaminista Abdallah Hamdok wanda ke ganawar da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya ce a halin yanzu ba zai iya daukar matakin dawo da huldar diflomasiyya tsakanin Sudan da Isra’ila ba.

Hamdok wanda aka nada kan mukamin firaminista bayan faduwar gwamnatin Omar Hassan Albashir, ya gana da Pompeo ne da ke ziyarar aiki irinta ta farko da wani jami’in diflomasiyyar Amurka ya kai a Khartum cikin shekaru 15 da suka gabata a wannan talata.

A lokacin ziyarar ce Mike Pompeo ya gabatarwa mahukuntan na Sudan bukatar ganin sun dawo da huldar diflomasiyya tsakanin kasar da Isra’ila, to sai dai martanin da Firaminista Hamdok ya mayar na matsayin koma-baya ga yunkurin da Amurkan ke yi don ganin cewa an samu karin kasashen larabawa da za su mayar da huldarsu da Isra’Ia ko baya ga Hadaddiyar Daular Larabawa.

To sai dai shugaban gwamnatin rikon kwaryar ya yi kira ga Amurka da kada ta alakanta wannan batu na Isra’ila da kokarin cire kasar daga cikin jerin kasashen da ke mara wa ta’addanci a duniya,

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.