Bakonmu a Yau

Tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko, kan nasarar kammala kakkabe Polio a Afrika

Sauti 03:39
Larabar nan ne WHO ta bayyana kawo karshen cutar ta Polio a Afrika.
Larabar nan ne WHO ta bayyana kawo karshen cutar ta Polio a Afrika. PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar a hukumance cewar nahiyar Afirka ta rabu da cutar polio bayan kwashe shekaru da dama ana yaki da ita wajen bada allurar rigakafi a kasashen duniya.Tun daga shekarar 1996 Hukumar Lafiya ta fara yaki da cutar polio wajen yiwa yara rigakafi abinda ya kaiga kare yara miliyan guda da dubu 800 daga zama guragu da kuma kare rayukan mutane 180,000.Dangane da wannan nasara mun tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, kuma ga tsokacin da yayi akai.