Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

WHO ta ce an kawar da cutar Polio a Afrika

Sauti 15:36
Jami'ai yayin bada allurar rigakafin cutar polio a arewacin Najeriya.
Jami'ai yayin bada allurar rigakafin cutar polio a arewacin Najeriya. PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya tayi shelar cewar Afirka ta rabu da cutar polio bayan kwashe dogon lokaci ana yaki da cutar a fadin duniya.Hukumar tace tayi nasarar kare yara miliyan guda da dubu 800 daga zama guragu, yayin da ceto rayukan mutane 180,000 wajen yaki da cutar.Yaya kuke kallon wannan nasara?Wane irin darasi ya dace Afirka ta koya daga wannan yakin ?Ta yaya kuke ganin Afirka zata yaki wasu cututtukan da suka rage ?