Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Dr Dauda Muhammad Kontagora kan sake zaben Akinwumi Adesina da bankin raya Afrika ya yi

Sauti 03:38
Shugaban bankin raya Afrika Akinwumi Adesina.
Shugaban bankin raya Afrika Akinwumi Adesina. Riccardo Savi / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / Getty Images via AF

Shugabannin Afirka sun sake zaben Akinwumi Adeshina a matsayin shugaban Bankin Raya kasashen Afirka domin yin wa’adi na biyu na karin shekaru 5.Taron shugabannin kasashen da akayi a Abidjan ya amince da cigaba da tafiya da Akinwumi sakamakon nasarorin da ya samu a shekaru 5 na farko duk da korafe korafen da akayi akan sa, wanda bincike ya wanke shi.Dangane da wannan nasara ta Adeshina, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki, Dr Dauda Muhammad Kontagora, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.