Mali-ECOWAS

ECOWAS ta baiwa sojin Mali wa'adin shekara 1 da su mikawa farar hula mulki

Hotunan taron shugabannin kasashen ECOWAS ta kafar bidiyon Internet kan kasar Mali.
Hotunan taron shugabannin kasashen ECOWAS ta kafar bidiyon Internet kan kasar Mali. © ECOWAS via REUTERS

Shugabannin kasashen Afrika ta yamma sun baiwa sojojin da suka yi juyin mulki a Mali, wa’adin shekara guda da su mikawa fararen hula mulki.

Talla

Matsayin da kasashen na ECOWAS suka dauka a jiya Juma’a yayin taronsu ta kafar bidiyo, ya zo ne bayan da sojojin na Mali suka saki tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Keita da suka tsare shi tun ranar 18 ga watan Agustan da muke, lokacin da suka aiwatar da juyin mulki.

Taron kasashen na ECOWAS ya bukaci sojin na Mali da su soma shirin aiwatar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisa cikin watanni 12.

Yayin jawabin rufe taron na ECOWAS shugaban kungiyar, zalika shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Muhammadu, yace sannu a hankali za su janye takunkuman da suka laftawa gwamnatin sojin kasar Mali, amma da sharadin amsa bukatar gaggauta mikawa farar hula mulki.

Yanayin da Mali ta tsinci kanta a ciki ya jefawa makotanta da kuma uwargijiyarta Faransa cikin fargaba, la’akari da tarin kalubalen kungiyoyin yan ta’adda, rikicin kabilanci da kuma matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI