Muhallinka Rayuwarka

Tasirin matsalolin tsaro kan noma a Najeriya

Sauti 19:48
Wasu manoma yayin gyaran shinkafar da suka girbe a jihar Benue dake Najeriya. 3/12/2019.
Wasu manoma yayin gyaran shinkafar da suka girbe a jihar Benue dake Najeriya. 3/12/2019. REUTERS/Afolabi Sotunde

Shirin Muhallinka Rayuwarka a wannan mako ya tattauna ne kan muhimman batutuwa guda biyu, da suka hada da bunkasa noman itaciyar Gawo a Najeriya, da kuma sha'anin tsaro, abinda ko shakkah babu ke da tasiri kan ayyukan noma a kasar, musamman a yankunan karkara.Ga dai masu bibiyar kafafen labarai sun sha jin rahotannin yadda masana ke bayyana fargabar fuskantar karancin abinci a wasu sassan Najeriya, sakamakon yadda matsalar tsaro ta dakatar da noman a yankunan arewa maso yammacin kasarda kuma arewa maso gabashi.