Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Samba Panza za ta nemi kujerar shugabancin kasar Afrika ta tsakiya

Catherine Samba Panza
Catherine Samba Panza Reuters

Catherine Samba Panza, shugabar rikon kwariyar Afrika ta tsakiya tsakanin shekara ta 2014 zuwa 2016 a jiya juma’a ta bayyana aniyar tsayawa takarar shugabancin kasar na watan Disembar shekarar bana.

Talla

Uwargida Samba Panza na kalon kanta a matsayin wacce ke da kwarewa da jajircewa wajen tafiyar da shugabancin kasar ,duk da rahotanni dake dada nuna ta yada ake fuskantar rashin tsaro a wasu yankunan kasar.

Tsofuwar Shugabar kasar ta dai karatu shara’a,ta na daga cikin mata na farko a yankin tsakiyar Afrika da suka rike babban mukami, ta kuma mika mulki ga Faustin Archange Touadera, mutumin da ya lashe zaben watan maris na shekara ta 2016,da kuma ake sa ran zai sake tsayawa takara a zaben na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.