Mali

Sojin Mali sun soke tattaunawa da kawancen 'yan adawa kan makomar kasar

Ismael Wague, kakakin gwamnatin sojin Mali a babban sansanin sojin dake Kati, dake wajen birnin Bamako. 26/8/2020.
Ismael Wague, kakakin gwamnatin sojin Mali a babban sansanin sojin dake Kati, dake wajen birnin Bamako. 26/8/2020. © Annie Risemberg/AFP

Gwamnatin sojin da suka yi juyin mulki a Mali ta dakatar da ganawar farko da suka shirya yi da kawancen ‘yan adawar kasa a jiya asabar, don tattaunawa kan makomar siyasar kasar, abinda yasa wasu fargabar ko an soma samun baraka tsakanin bangarorin ne tun ba a je ko ina ba.

Talla

Rahotanni sun ce maimakon tattaunawa da kawancen ‘yan adawar, sojin na Mali sun gana ne da Mahmoud Dicko, malamin da ya jagoranci zanga-zangar adawa da tsohon shugaba Kieta kafin kawo karshen gwamnatinsa a ranar 18 ga Agustan da muke.

A makon da ya kare, kungiyar kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS ta kakabawa gwamnatin sojin kasar ta Mali takunkuman dakatar da cinikayya da ita, kana da rufe mata iyakokin kasashe makofta, domin tilastawa sojin gaggauta mikawa farar hula mulki.

Ranar Juma'a 28 ga watan Agusta, kungiyar ta ECOWAS, ta baiwa sojojin na Mali, wa’adin shekara guda da su mikawa fararen hula mulki.

Matsayin da kasashen na ECOWAS suka yayin taronsu ta kafar bidiyo, ya zo ne bayan da sojojin na Mali suka saki tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Keita da suka tsare shi tun ranar 18 ga watan Agustan da muke, lokacin da suka aiwatar da juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.