Tanzania

'Yan adawar Tanzania sun zargi gwamnati da yin coge a rijistar 'yan takara

Tundu Lissu jagoran 'yan adawa dake takarar shugabancin kasar Tanzania a zaben watan Oktoba.
Tundu Lissu jagoran 'yan adawa dake takarar shugabancin kasar Tanzania a zaben watan Oktoba. CHADEMA Tanzania/twitter.com

'Yan adawa a Tanzania sun zargi gwamnati da yin coge yayin yiwa ‘yan takararsu rijistar shiga takara a zabukan kasar dake tafe a karshen watan Oktoba.

Talla

Jagoran ‘yan adawa a kasar ta Tanzania Tundu Lissu, yace yanzu haka gwamman ‘yan takara ne hukumar zaben kasar ta ki baiwa damar shiga zaben dake tafe, domin rashin adalci kawai, ba tare da kwararan dalilai ba.

A cewar Lissu ‘yan adawa na da jumillar ‘yan takara dubu 3 da 754 a zaben kananan hukumomi amma hukumar zabe ta yi watsi da kashi 30 daga ciki, sai kuma ‘yan takarar kujerun majalisar kasar 53 da aka zaftare daga cikin 244.

A watan jiya Tundu Lissu ya koma Tanzani daga Belgium, inda ya shafe shekaru yana gudun hijira, bayan tsallake riiya da baya a shekarar 2017, lokacin da ‘yan bindiga suka yi yunkurin halaka shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.