Chadi

Chadi: Mutane 10 sun mutu a rikicin manoma da makiyaya

Rikicin manoma da makiyaya ya sake barkewa a kudu maso yammacin kasar Chad.
Rikicin manoma da makiyaya ya sake barkewa a kudu maso yammacin kasar Chad. AFP Photo/Amaury HAUCHARD

Akalla mutane 10 aka kashe a Chadi sakamakon rikicin manoma da makiyaya kudancin kasar, kuma dukkanin wadanda aka kashe makiyaya ne Larabawa.

Talla

Mai gabatar da kara na Moundou dake yankin Logone, Brahim Ali kolla, yace rikicin ya barke ne bayan da kabilun makiyaya suka zargi manoma da satar shanu, bayan da suka gano wata saniya da aka sace a daya daga cikin gonakin yankin.

Bayan gano saniyar ce, makiyayan suka tura wakili domin karbota, amma manoman suka kashe shi, zalika suka kara da kaiwa makiyayan farmaki a lokacin da suke jana’izar dan uwan nasu da aka halaka.

Bayaga matsalolin mayakan Boko Haram dai, kazamin rikicin manoma da makiyaya larabawa mafi akasari kan mallakar filaye a kudu maso yammaci ke kan gaba wajen ciwa al’ummar Chadi tuwo a kwarya.

Yanzu haka dai jami’an tsaron kasar ta Chadi sun cafke mutane 43 dake da hannu a rikicin da ya salwantar da rayuka.

Alhaji Mustapha Ibrahim shi ne sarkin Hausawan Djamena wanda yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, yayi tsokaci kan halin da ake ciki dangane da rikicin manoma da makiyayan a kasar ta Chadi.

Alhaji Mustapha Ibrahim sarkin Hausawan Djamena kan rikicin manoma da makiyayan a Chadi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.