Duniya

Donald Trump ya ziyarci Kenosha

Donald Trump ya ziyarci Kenosha
Donald Trump ya ziyarci Kenosha REUTERS/Leah Millis

Shugaban Amurka Donald Trump ya kai wata ziyarar ba zata yankin Kenosha na Wisconsinyankin da mutane suka shiga tarzoma da ta haifar da  muhawara sosai bayanda wani dan sanda farar fata ya harbi wani bakar fata Jacob Blake gaban ‘ya’yansa 3.

Talla

Wannan dai ba shine karon farko ban a kisan bakar fata da ‘Yan Sandan Amurka ke yi domin a dan tsakanin nan an sami irin haka akalla 3 a kasar.

Shugaban Amurka Donald Trump ya nemi ya gana da iyalan Jacob Blake,wandada nan take suka bayyana adawar su ga tayin Shugaban na Amurka tareda bukatar lauya mai kare su ya kasance a wannan ganawa da Shugaban na Amurka.

Yayinda da Shugaban Amurka ke ci gaba da fuskantar suka daga yan kasar bisa danganta shi da mai sakaci wajen daukar matakai don kawo karshen muzgunawa bakar fata a Amurka.

Mun nemi ji daga Abdulrahman Dandi Abarshi mazaunin Indiana ko yaya suka ji da wannan al'amari.

Donald Trump ya ziyarci Kenosha

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.