Afrika

Ana zargin sojojin da kisan farraren hula a Nijar

Wasu daga cikin yankunan dake fama da rashin tsaro a yankin Tillabery daf da kan iyaka da Burkina Faso
Wasu daga cikin yankunan dake fama da rashin tsaro a yankin Tillabery daf da kan iyaka da Burkina Faso RFI/Sayouba Traoré

A Jamhuriyar Nijar,wani bincike daga wata kungiya mai zaman kan ta da aka sani da CNDH na nuni cewa dakarun Nijar dake fada da yan ta’ada sun hallaka farraren hula da ba su san hawa bale sauka ba a yankin Tillabery.

Talla

Abdoulaye Seydu shugaban kungiyar ta CNDH ya bayyana cewa sun gano kusan ramuka guda uku da aka bine gawarwakin mutane 71,akasarin su farraren hula, inda aka kuma gano cewa an yi amfani da makamai da suka hada da wuka da bindiga wajen halaka su.

An dai gudanar da wannan bincike kama daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa 6 ga watan yuli na shekarar bana,tareda gundumuwar kungiyoyi dake kare hakokin bil adam.

Wasu rahotani na tabbatar da cewa biyo bayan tono gawarwakin ,an gano cewa kowanen su hannayan sa a daure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.