Mali

An fitar da tsohon shugaban Mali zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa

Tsohon Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita
Tsohon Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita Ludovic Marin /Pool via REUTERS

Tsohon shugaban ma’aikatan fadar hambararren shugaban Mali Ibrahim Boubacar Kieta, Mamadou Kamara yace an fita da tsohon shugaban kasar zuwa birnin Abu Dhabi a Hadaddiyar Daular Larabawa a jiya asabar, domin kulawa da lafiyarsa.

Talla

Tun Talatar makon da ya kare ne dai aka kwantar da tsohon shugaba Kieta a wani asibiti dake birnin Bamako, kwanaki 6 bayan sakinsa da sojin kasar suka yi daga tsarewar da suka masa, ranar 18 ga watan Agusta, lokacin da suka yi juyin mulki.

A jiya asabar din kuma aka soma tattaunawa tsakanin gwamnatin sojin na Mali da wakilan jam’iyyu da sauran kungiyoyin a birnin Bamako, kan shirin sake mikawa farar hula mulki.

Sai dai rahotanni sun ce sa’o’i kalilan bayan soma ganawar gamayyar kungiyar ‘ayn adawa ta M5-RFP da ta soma jagorantar zanga-zangar kin jinin tsohon shugaba Kieta, ta zargi gwamnatin sojin kasar ta maida ta saniyar ware a tattaunawar da ta soma da farar hula, abinda ya sanya ta kaddamar da wata sabuwar zanga-zangar, matakin da ya tilasta dakatar da taron na wucin gadi.

Yau alahadi taron sojin da farara hular na Mali ke cigaba da gudana, zalika za a dora kansa a sassan kasar cikin mako mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.