Jami’an tsaron Spain sun ceto ‘yan ci rani kusan 300 a gabar ruwan Morocco

Bakin haure a tekun Mediterraniya
Bakin haure a tekun Mediterraniya MV Louise Michel/Handout via REUTERS

Jami’an tsaron gabar ruwan Spain sun ceto ‘yan ci rani kusan 300 da gawar mutum guda daga nutsewa cikin teku a gaf da tsibirin Canary.Wannan dai itace tawaga ta baya bayan nan da ta isa Spain, a cigaba da kokarin da ‘yan ci ranin ke yin a kwarara zuwa nahiyar Turai.

Talla

‘yan ci rani 283 ne jami’an gabar ruwan na Spain suka ceto daga cikin kananan jirage akalla 8, a daidai lokacin da suke cikin barazanar nutsewa cikin tekun Atlantic a gaf da tsibirin Canary dake yammacin kasar Morocco, bayan tagayyarar da suka yi, a kokarinsu na tsallakawa cikin Turai.

Yanzu haka dai karin ‘yan ci ranin kusan 300 na zaune ne a wasu sabbin sansanonin wucin gadi dake tashar jiragen ruwan Gran Canaria a kasar ta Spain, sakamakon cikar kwarin da tsaffin sansanonin suka yi.

Tsallaka teku daga yammacin Afrika zuwa tsibiran kasar Spain na tattare da matukar hadari, sai dai duk da haka yawan ‘yan ci ranin dake bin hanyar don tsallaka tekun Atlantic ya karu a baya bayan nan, sakamakon tsaurara sintiri kan iyakokin tekun Mediteraniya da kasashen Turai suka yi.

Hukumar kula da yan gudun hijira ta duniya IOM tace, Akalla ‘yan ci rani 239 suka mutu tsakanin 1 ga watan janairun wannan shekara zuwa 19 ga Agustan da yak are, yayinda suka yi kokarin tsallaka tekun Atlantic don isa tsibirin Canary na Spain, sabanin 210 da suka mutu a shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.