Afrika-Ecowas

Arangama ta kaure tsakanin yan Sanda da masu zanga-zanga a Bamako

Tattaunawa tsakanin sojojin Mali da kungiyoyin siyasa da na fara hula a Bamako
Tattaunawa tsakanin sojojin Mali da kungiyoyin siyasa da na fara hula a Bamako David Baché/RFI

An samu arrangama tsakanin ‘yan sandan Mali da masu zanga-zanga a birnin Bamako, wadanda ke neman sojin kasar da su gaggauta mikawa farar hula mulki yayinda wasu daga cikin mutan kasar ke fatan sojoji su ci gaba da rike madafan iko.

Talla

Sabon gangamin da mabiya kawancen da suka jagoranci zanga-zangar kin jinin tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Kieta na zuwa ne a dai dai lokacin da aka soma tattaunawa da wakilan jami’yyu, kungiyoyin fararen hula da kuma shugabannin gwamnatin soji da suka yi juyin mulki, kan shirin sake komawa mulkin Dimokaradiya.

Kusan wata daya kenan da sojoji suka kiffar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita,tsofuwar gwamnatin da ta fuskanci bore sabili da gazawa wajen magance matsalar tsaro da kuma samarwa yan kasar kayen more rayuwa.

Kungiyar Ecowas ta umurci gwamnatin sojan kasar da ta gaggauta mika mulki ga farar hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.