Najeriya

Rarara ya ce ba zai kara yiwa shugaba Buhari waka kyauta ba

Dauda Kahutu Rarara Shaharerren mawakin 'yan siyasar Najeriya musamman shugan kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyan APC
Dauda Kahutu Rarara Shaharerren mawakin 'yan siyasar Najeriya musamman shugan kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyan APC Aminiya

Adadin mutanen da suka tallafawa Rarara ta cikin asusun tara kudin wakar Buhari sun kai 60.A ranar laraba ne fitaccen mawakin siyasar a Najeriya yace ba zai kara yiwa shugaba Buhari waka kyauta ba har sai masoyan shugaban sun tallafa da naira dubu dubu.

Talla

Matakin na Rarara dai ya zamo abun tattaunawa a shafukan sada zumunta a Najeriya musaman arewacin kasar , koda dai Dauda Kahutun yace kada fa ayi zaton ko ya samu matsala ne da Shugaba Buhari, yana mai nanata cewa akwai tabbacin ba masoyan Buhari ne ke sukar sa ba illa dai yan ta fadi gasassa.

A yan kwanakin nan dai shugaban Najeriyar na shan caccaka a shafukan sada zumunta tun bayan matakin Karin kudin man fetir da lantarki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI