Najeriya

Na’urorin tantance masu kada kuri’a sun kone a Ondo

Wasu daga cikin jami'an hukumar zaben Najeriya
Wasu daga cikin jami'an hukumar zaben Najeriya REUTERS/Tife Owolabi

Hukumar zaben Najeriya tace na’urorin Card Readers na tantance masu kada kuri’a sama da dubu 5 sun kone, a gobarar da ta tashi a ofishinta dake garin Akure a Jihar Ondo.

Talla

Yayin ganawa da manema labarai a jiya Juma’a, kwamishinan zaben jihar ta Ondo, Ambassada Rufus Akeju, yace gobarar ta soma ne da misalign karfe bakwai da rabi na ranar alhamis, abinda ya kai ga kone na’urorin na Card Readers dubu 5 da 141.

Iftila’in gobarar ya auku ne yayinda ya rage makwanni a yi zaben gwamnan jihar ta Ondo a ranar 10 ga watan Oktoba mai zuwa, abinda ya haifar da fargabar ko lamarin zai shafe zaben dake tafe.

Sai dai shugaban hukumar zaben yace gobarar ba za ta shafi ranar da aka tsaida na gudanar da zaben gwamnan jihar at Ondo ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI