Najeriya

Najeriya:Rarrabuwan kawunan al'umma ya fi kamari Mulkin a Buhari - Soyinka

Wole Soyinka, shahararren marubuci a Najeriya.
Wole Soyinka, shahararren marubuci a Najeriya. PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Fitaccen marubucin Najeriya Farfesa Wole Soyinka ya ce kasar bata taba ganin yadda aka samu rarrabuwar kawunan jama’a ba kamar yadda ake gani yanzu haka a karkashin jagorancin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Talla

Wata sanarwar da ya rabawa manema labarai ta ce ‘yan Najeriya sun fidda tsammani cewar gwamnatin Buhari za ta iya tabbatar da ci gaba da dorewar kasar a matsayin kasa guda.

Soyinka ya ce 'yan Najeriya da dama sun yanke hukuncin cewar gwamnatin bata fahimci mafi karancin bukatar daidaita kasar a matsayin ta zamani kuma wacce za ta samar wa kan ta cigaban da ake bukata ba.

Marubucin ya ce kasar ta rarrabu yadda ba’a taba gani a baya ba, kuma alhakin hakan ya rataya ne akan shugaban kasa Muhammadu Buhari kan irin manufofin da yake gabatarwa da kuma yadda ake tafiyar da kasar.

Soyinka ya ce kowa ya san lokacin da shugaban kasa Buhari ke sharar barci yayin da makiyaya ke kashe jama’a suna musu fyade da kuma raba su da muhallan su, yayin da ake rokon sa da ya ziyarci yankunan da suka gamu da kashe kashe, inda baya daukar mataki sai bada shawarar jama’a su zauna lafiya da masu kai musu hari.

Fitaccen marubucin ya ce shugaban ya gaza daukar mataki kan Sufeto Janar na 'yan sanda  da yaki amsa umurnin sa domin zama a yankin da ake fama da tashin hankali.

Farfesa Soyinka wanda ya ce duk da cewa ba ya shiri da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, yana goyan bayan kalamanda ya yi cewar Najeriya ta kama hanyar rugujewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI