Senegal

Sojojin Senegal 200 sun harbu da coronavirus

Shugaban Senegal Macky Sall
Shugaban Senegal Macky Sall RFI

Gwamnati Kasar Senegal ta ce akalla sojojin ta sama da 200 suka harbu da cutar korona bayan komawar su gida daga kasar Gambia inda suka yi akin samar da tsaro a karkashin kungiyar ECOWAS.

Talla

Rahotan farko ya ce sojoji sama da 100 suka harbu da cuta daga cikin sama da 600 da suke cikin tawagar da ke aikin samar da tsaron.

Rundunar sojin Senegal da ma’aikatar lafiyar kasar sun ce yanzu haka an killace sojojin 208 a kauyen Guereo dake da nisan kilomita 60 daga birnin Dakar inda ake kula da su.

Yan kasar Senegal 14,529 suka kamu da cutar korona, kuma 298 daga cikin su sun mutu, yayin da 3,428 suka kamu da cutar a Gambia, kuma 105 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.