Afrika

Darajar Naira ta sake faduwa kan dalar Amurka

Takardar kudin Nairan Najeriya
Takardar kudin Nairan Najeriya Getty Images

Darajar Naira ta sake faduwa kan dalar Amurka a canjin kasuwar bayan fage, inda a yanzu ta koma naira 460.Wannan kuwa na zuwa duk da cewar, babban bankin Najeriya ya koma cigaba da saidawa cibiyoyin ‘yan canjin kudaden na BDCS.

Talla

Bayanai sun ce ranar 7 ga watan Satumban da muke, bankin Najeriyar ya saida dala miliyan 51 ga cibiyoyin ‘yan canji na BDCS dubu 5 da 180, lokacin da ya cigaba da shirinsa na kokarin daga darajar Naira.

Yanzu haka dai a hukumance nairar Najeriya 380 ke daidai da dala 1 kudin Amurka, bayan sake karya darajar Nairar da gwamnatin Najeriya ta yi.

Yan kasuwa na dada nuna fargaba ganin halin da suka fada duk da cewa iyakokin kasar na rufe,lamarin da ya haifar da tsadar kayaki a kasuwani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.