Mali-ECOWAS

ECOWAS na so farar hula ya jagoranci gwamnatin wucin gadin Mali

Shugabannin kasashen yammacin Afrika a yayin taro kan Mali a Ghana.
Shugabannin kasashen yammacin Afrika a yayin taro kan Mali a Ghana. © ECOWAS via REUTERS

Shugaban Ghana Nana Akufo Addo ya ce jagororin kasashen Afrika na fatan ganin an kafa gwamnatin wucin gadi a kasar Mali cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, bayan tattaunawar da suka yi da sojojin da suka hambare gwamnatin kasar.

Talla

Nana Akufo-Addo, wanda a halin yanzu shine shugaban kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, ya shaida wa manema labarai cewa bukatarsu ita ce farar hula ya jagoranci gwamnatin wucin gadi da za ta mika mulki ga zababben shugaba a kasar.

Ya kara da cewa da zarar an kafa gwamnatin da al’umma Mali suka  yi na’am da ita, kungiyar ECOWAS za ta cire dukkannin takunkuman da ta sanya wa kasar.

Akufo-Addo ya ce nan da mako guda mai shiga tsakani na kungiyar ta ECOWAS zai yi tattaki zuwa birnin Bamako, don a awaitar da kudirorin da aka zartas.

ECOWAS ta kakaba wa Mali jerin takunkumai da suka hada da rufe iyakoki, da haramta kasuwanci da sauransu, bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita.

Kungiyar ta baiwa sabuwar gwamnatin sojin wa’adin zuwa Talata mai zuwa ta bayyana farar hula a matsayin shugaba da Firaminista da za su jagorancin gwamnatin wucin gadi.

Jagoran gwamnatin mulkin sojin Mali, Assimi Goita, ya halarci taron tattaunawar a Ghana, a tafiyarsa zuwa kasar waje ta farko tun da ya kifar da gwamnatin farar hula.

Juyin mulkin na watan da ya gabata, wanda shine na hudu tun da kasar ta samu ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Faransa a shekarar 1960, ya zo ne bayan jerin zanga zanga da aka shafe watanni ana yi sakamakon gazawar shugaba Keita wajen kawo karshen rikicin ‘yan ta’adda da ya addabi kasar tun shekarar 2012.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.