WHO-Lafiya

Korona ta kashe masu taimakawa likitoci sama da 1.000

Daya daga cikin jami'an kiwon lafiyar da ke yaki da coronavirus
Daya daga cikin jami'an kiwon lafiyar da ke yaki da coronavirus AFP Photos/Eduardo Soteras

Hukumar dake kula da masu taimakawa aikin likita ta duniya tace akalla ‘ya'an ta sama da 1,000 suka mutu a kasashen duniya yayin kula da masu dauke da cutar korona.

Talla

Sanarwar da hukumar dake da cibiya a Geneva ta gabatar, ya bayyana lamarin a matsayin abin tada hankali, inda ta zargi gwamnatocin kasashen duniya da gazawa wajen daukar matakan da suka dace domin kare ma’aikatan lafiyar.

Kungiyar dake da ‘ya'a sama da miliyan 20 a kasashen duniya 130 tace daga barkewar annobar zuwa ranar 14 ga watan Agusta ta tabbatar da mutuwar ‘yayan ta 1,097 a cikin kasashe 44, kuma 351 sun mutu ne a Brazil, yayin da 212 suka fito daga Mexico.

Kungiyar Amnesty International tace ma’aikatan lafiya sama da 7,000 suka mutu sakamakon annobar, yayin da kungiyar masu taimakawa likitocin ke cewa adadin na iya fin haka, saboda matsalar tattara bayanai.

Shugaban kungiyar yace bayanan da suka samu sun nuna cewar ma’aikatan lafiya 572,478 suka kamu da cutar korona a kasashe 32.

Ya zuwa yanzu cutar ta kashe mutane 936,095 a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI