Kotun Faransa ta daure Lamine Diack shekaru 4
Wata Kotu a Faransa ta daure tsohon shugaban hukumar kula da guje-guje ta duniya Lamine Diack shekaru 4 a gidan yari da kuma tarar Dala 600,000 saboda samun sa da rufa rufa kan yadda yan wasan Rasha suka dinga amfani da miyagun kwayoyi.
Wallafawa ranar:
Diack mai shekaru 87 wanda dan kasar Senegal ne ya jagoranci kungiyar na shekaru 16 kafin tuhumar da aka masa.
Mai shari Rose-Marie Hunault a Paris tace kauda kan da Lamine Diack yayi ya haifar da matsaloli sosai a kokarin da duniya ke yi na yaki da miyagun kwayoyi a bangaren wasanni.
Hunault tace duk da hukuncin daurin da ta yankewa tsohon jami’in wasannin, da alama ba za’a kai shi gidan yari ba saboda yawan shekarun sa.
Lamine Diack wanda yaki amincewa da hukuncin yace zai daukaka kara.
Kotun ta kuma samu dan Diack, Papa Massata da laifi kan badakalar inda ta daure shi shekaru 5 a gidan yari da kuma tarar euro miliyan guda saboda rawar da ya taka lokacin da ya jagoranci sashen kasuwanci na hukumar IAAF.
Lamine Diack ya jagoranci hukumar IAAF daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2015 kafin Sebastian Coe na Birtaniya ya maye gurbin sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu