Najeriya - kidnappers

Najeriya: Masu satar mutane sun fara kisa ko da an biya kudin fansa

kwatance na 'yan bindiga da suka addabi al'ummar arewacin Najeriya.
kwatance na 'yan bindiga da suka addabi al'ummar arewacin Najeriya. Solacebase

A Najeriya ta’asar da masu satar mutane don karbar kudin fansa ke yi, musammam ma a yankin arewacin kasar yana ci gaba da ci wa al’umma tuwo a kwarya, saboda sau da dama suna nuna rashin kwarewa ta wajen kisan wadanda suka sata, ko da an biya su kudin fansa, kamar yadda ya faru a jihar Katsina, inda wasu masu satar mutane suka kashe wani jami’in hukumar DSS duk da cewa an biya su zunzurutun kudi.

Talla

Sadiq Abdullahi Bindawa, shine jami’in hukumar tsaro ta DSS da da ya gamu da ajalinsa a hannun ‘yan bindiga masu satar mutane don kudin fansa a jihar Katsina ta Najeriya, duk da cewa wadannan mutane sun karbi kudi wuri na gugar wuri har naira miliyan 5 a matsayin kudin fansarsa.

A cewar majiyoyi na kusa da iyalansa, Bindawa ya ziyarci Katsina da dansa mai shekaru 4 a ranar Juma’ar da ta gabata da zummar yin hutun karshen mako da ‘yan uwansa ne wannan bakin al’amari ya auku.

Wani na kusa da iyalin, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce masu satar mutanen sun nemi a bada miliyan 13 ne tun da farko, amma bayan ciniki da aka buga suka sauko zuwa miliyan 5, amma kuma ba su bar shi da ransa ba.

Ya ce duk da cewa sun shaida wa ‘yan sanda abin da ya auku, babu wani tasiri da hakan ya yi.

Wani mai sharhi a kan tsaro da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce irin wannan dabi'a da masu satar mutane a arewacin Najeriya suka dauka, na kisan wadanda suka sace ko da an biya su kudin fansa, ka iya taurara zukatan al'umma nan ba da jimawa ba, inda har za su ga rashin amfanin biyan kudin fansa, lamarin da zai iya sa su yi kukan kura su shiga farautar barayin a inda suke buya, wanda zai kai ga karshen 'yan tsageran.

Satar mutane don karbar kudin fansa ya dauki wani salo mai tayar da hankali a arewa maso yammacin Najeriya, inda sau dama barayin mutanen ke kisan wadanda suka sata ko da kuwa an biya kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI