Mali

Tsohon shugaban kasar Mali, Moussa Troare ya rasu yana da shekaru 83

Tsohon shugaban Mali, Moussa Traoré.
Tsohon shugaban Mali, Moussa Traoré. AFP/Kazuhiro Nogi

Tsohon shugaban kasar Mali, Moussa Traore, wanda ya jagoranci kasar daga shekarar 1968 zuwa 1991 da aka mai juyin mulki ya rasu a gidansa da ke babban birnin kasar Bamako yana da shakaru 83.

Talla

A matsayinsa na matashin soji mai mukamin Laftanar a shekarar 1968, Traore ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin farar hula ta Modibo Keita, shugaban kasar na farko bayan samun yancin kai.

Bayan nasarar juyin mulkin ne Traore ya dare karagar mulkin kasar.

A shekaru 22 da ya yi yana jagorancin Mali, an yi zargin sa da kamawa tare da tsare ‘yan adawa, da kuma yin dirar mikiya kan masu zanga zanga, sannan wasu sun dora alhakin mutuwar shugaban kasar na farko, Modibo Keita, wanda ya mutu a gidan yari a kansa.

Sai dai Keita ya yi fice a wajen iya diflomasiyya. A matsayinsa na shugaban kungiyar hada kan Afrika a lokacin, wato OAU, ya taka mahimmiyar rawa wajen warware rikici tsakanin Mauritania da Senegal a shekarar 1989.

A shekarar 1990, Traore ya cimma yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan tawayen Tuareg da suka dau makamai don yakar gwamnati.

A shekarar 1991 ne dai sojojin da ya tura don su dakile zanga zangar da ake na neman kafuwar dimokaradiyya suka juya kansa, suka yi wani mummunan juyin mulki da ya yi sanadin lakume rayukan mutane 200, ya kuma jikkata 1,000.

An yanke mai hukuncin kisa a shekarar 1993, sannan aka yanke mai makamancin hukuncin da shi da matarsa a shekarar 1999.

An rage tsaurin hukuncin zuwa daurin rai da rai, kana a shekarar 2002 aka yi mai afuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.