Najeriya

Unicef ta soki Najeriya kan hukuncin Islama

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Solacebase

Majalisar Dinkin Duniya ta soki matakin da Najeriya ta dauka na daure wani matashi mai shekaru 13 Omar Faruk shekaru 10 a gidan yari saboda samun sa da laifin batanci ga addinin Islama.

Talla

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar ta bayyana matakin da hukumomin Najeriya suka dauka wanda suka ce ya sabawa ‘yancin kare hakkokin yara kanana da kuma yi musu adalci wanda Najeriya ta rattaba hannu a kai a shekarar 1991.

Wakilin hukumar UNICEF a Najeriya Peter Hawkins ya bukaci gwamnatin tarayya da ta Jihar Kano da su gaggauta sake nazari kan hukuncin da aka yankewa Faruk na daurin shekaru 10.

Jihohin Arewacin Najeriya da dama sun kaddamar da shari’ar Musulunci bayan komawa mulkin dimokiradiya a shekarar 1999, inda ake yiwa Musulmi shari’a kamar yadda dokokin addini suka tanada.

Ita dai wannan kotu bata yiwa wanda ba Musulmi ba shari’a sai dai idan ya bukaci haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI