Uganda

Jami'an tsaron Uganda na farautar wasu fursinoni da suka tsere daga kurkuku

Hukumomin kasar Uganda sun kaddamar da samame domin gano wasu fursinoni sama da 200 da suka tsere daga wani gidan yari, bayan arangamar da suka yi da masu tsaron su wanda yayi sanadiyar hallaka mutane 4.

Wasu jami'an tsaron Uganda.
Wasu jami'an tsaron Uganda. Reuters/James Akena
Talla

Fursinonin sun yi nasarar kwashe makamai daga rumbun gidan yarin da ke Moroto da ke da nisan kilomita 460 daga birnin Kampala kafin su tsere zuwa tsaunukan da ke yankin.

Kakakin jami’an gidan yarin kasar Frank Baine ya ce an kashe soja guda da fursinoni 3 lokacin arangamar, yayin da aka baza sojoji da 'yansanda da jiragen sama domin farautar wadanda suka gudu.

Kwamishinan da ke kula da jami’an gidan yarin Johnson Byabashaija ya bayyana wasu daga cikin firsinonin da suka tsere a matsayin masu hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI