Habasha

'Yan bindiga sun kashe mutane da dama a Habasha

Rikicin kabilanci ya ta'azzara a Habasha
Rikicin kabilanci ya ta'azzara a Habasha STRINGER / AFP

Rahotanni daga Habasha sun ce wasu 'yan bindiga sun kashe mutane sama da 30 a yankin Metakal da ke Lardin Benishangul-Gumuz, a ci gaba da tashin hankalin da ake samu a kasar.

Talla

Wani babban jami’in adawa Desalegn Chane na Jam’iyyar Amhara ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Reuters cewa, an kai harin ne tsakanin ranakun 6 zuwa 13 na wannan wata, kuma cikin wadanda aka kashe har da mata da yara kanana.

Desalegne ya ce 'yan bindigar sun kama wasu manoma ne da iyalansu, inda suka kai su wata makarantar firamare, inda suka sanya musu ankwa a hannu, kana suka harbe su daya bayan daya.

Firaministan kasar Abiy Ahmed ya shaida wa taron majalisar ministocinsa cewa, hukumomin tarayya da na shiyoyi na nazari kan tabarbarewar tsaron da ake ci gaba da fuskanta, musamman akan iyakokin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.