Amurka-Iran

Afrika ta Kudu ta musanta zargin Amurka na shirin kisan jakadiyarta a Pretoria

Lana Marks, jakadiyar kasar Amurka a Afrika ta Kudu.
Lana Marks, jakadiyar kasar Amurka a Afrika ta Kudu. Larry Bussaca / Getty Images / AFP

Hukumomin tsaro a Afrika ta Kudu sun ce babu kamshin gaskiya a zargin da Amurka ke yiwa Iran na yunkurin kashe jakadiyarta dake birnin Pretoria Lana Marks.

Talla

A farkon wannan mako, kafafen yada labaran Amurka suka ce sun jiyo daga wasu manyan gwamnatin kasar cewa, Iran ta tsara kashe jakadiyyar kafin gudanar da zaben shugabancin Amurka da za a yi cikin watan Nuwamba mai zuwa.

A cewar majiyar kafafen yada labaran, Iran ta shirya kashe jakadiya Lana Marks a matsayin fansa dangane da kisan da Amurka ta yi wa janar Qassem Soleimani a birnin Bagadaza.

Sai dai kakakin hukumar ‘yan sandan ciki ta Afirka ta Kudu Mava Scott, ta ce binciken da hukumar ta gudanar bai gano wani abu mai kama da hakan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.