Habasha

Habasha na tuhumar jagoran adawar kasar da laifukan ta'addanci

Guda cikin jagororin 'yan adawa a Habasha  Jawar Mohammed.
Guda cikin jagororin 'yan adawa a Habasha Jawar Mohammed. HAILESELASSIE TADESE / AFP

Gwamnatin Habasha ta shigar da karar Jawar Mohammed gaban kotu, daya daga cikin jagororin ‘yan adawar kasar da take tuhuma da aikata laifukan ta’addanci da cin amanar kasa.

Talla

Tun cikin watan Yuni jami’an tsaro suka kame Jawar dan kabilar Oromo tare da mukarrabansa, yayinda yake jagorantar zanga-zangar adawa da gwamnati, biyo bayan kisan gillar da aka yiwa fitaccen mawaki Haacaaluu Hundeessaa da suka fito daga kabila daya.

Yanzu haka dai Mohammed Jawar da ya mallaki gamayyar kafafen yada labaran Oromiya Media Network tare da abokan gwagwarmayarsa 22, na fuskantar tuhumar, karya dokokin yaki da ta’addanci, mallakar makamai da kuma karya wasu dokoki da suka shafi kafofin sadarwa.

Ofishin ministan shari’ar Habasha ya ce a ranar litinin dukkanin wadanda ake tuhumar za su gurfana gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.