Kamaru

Kamto zai jagoranci zanga-zangar adawa da Paul Biya a makon gobe

Maurice Kamto jagoran 'yan dawa a Kamaru na jam'iyyar MRC yayin taron manema labarai a birnin Yaounde.
Maurice Kamto jagoran 'yan dawa a Kamaru na jam'iyyar MRC yayin taron manema labarai a birnin Yaounde. REUTERS/Zohra Bensemra

Jagoran ‘yan adawar Kamaru Maurice Kamto, ya bukaci al’ummar kasar da su amsa kiran gagarumar zanga-zangar adawa da gwamnati da zai jagoranta ranar talata a makon gobe, domin matsawa shugaba Paul Biya lamba, wajen tsagaita wuta a yankunan kasar masu amfani da turancin Ingilishi.

Talla

A watan janairun shekarar 2019, jami’an tsaron kamaru suka tsare Kamto tsawon watanni 9, bayan da ya jagoranci zanga-zangar adawa da sakamakon zaben shugabancin kasar na shekarar 2018, wanda ya sha kaye a hannu shugaba Paul Biya.

Bayaga neman zaman lafiya a yankunan masu amfani da turancin Ingilishi, wata karin bukatar ‘yan adawar na Kamaru ita ce yiwa dokokin zaben kasar kwaskwarima.

Cikin sanarwar baya bayan nan, jagoran ‘yan adawar na Kamaru Maurice Kamto da magoya bayansa suka sha alwashin jagorantar waa gagarumar zanga-zangar ta neman tilastawa shugaba Biya yin murabus, muddin yaki amsa jerin bukatun da suka gabatar masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.