Uganda

Jami'ar Makerere dake Uganda ta kone

Jami'ar Makerere dake Kampala  na kasar Uganda
Jami'ar Makerere dake Kampala na kasar Uganda Wikimedia / Eric Lubega and Elias Tuheretze

Rahotanni daga birnin Kampala na kasar Uganda na cewa gobara ta tashi a babbar Jami'ar kasar, daya daga cikin Jami'oin da suka fi dadewa a nahiyar Africa, Makerere University.

Talla

‘Yan Sandan kasar sun gaskata cewa gobarar ta lalata gine-ginen Jami'ar.

A cewar Mukaddashin kakakin ‘yan sandan Kampala Luke Oweyesigire gobarar ta yi barnar gaske, kuma ana gudanar da cikakken binciken gano musabbabin gobarar.

Mukaddashin shugaban Jami'ar Farfesa Barnabas Nawangwe ya bayyana cikin sakon tweeter cewa Jami'ar ta tafka hasara maras misaltuwa, domin sashen kula da harkokin mulki ya kone sosai.

A shekara ta 1922 aka kafa Jami'ar a matsayi makarantar koyon sana'oi kuma ya zuwa yanzu akwai dalibai sama da 35,000 da wasu dalibai dake karatun manyan Digirori 3,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI