Chadi

Mayakan Boko Haram sun halaka sojin Chadi 10

Sojojin kasar Chadi yayin atsaye a yankin Atar, dake Mauritania.
Sojojin kasar Chadi yayin atsaye a yankin Atar, dake Mauritania. US. Army/Sgt. Steven Lewis

Mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Chadi 10, bayanda suka yi musu kwanton bauna a lokacin da sojin suka kaiwa sansaninsu farmaki a yankin Tafkin Chadi.

Talla

Yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na AFP, sakataren gwamnatin yankin na Tafkin Chadi Saddik Khatir yace wasu sojojin bakwai sun jikkata yayin arrangamar.

Sai dai bayan tuntubar kakakin sojin na Chadi Azem Mbermandoa da AFP yayi, bada tabbacin samun nasarar rusa sansanin mayakan na Boko Haram kakakin yayi, ba tare da tabbatar da alkaluman dakarun da suka rasa ba.

Cikin watan Afrilun wannan shekara, shugaban Chadi Idris Deby ya zargi kasashen da ke fama da matsalar Boko Haram da nade hannayensu, inda suka bar Chadi kadai na yaki da mayakan kungiyar.

A waccan lokacin kuma Deby ya gargadi kasashen da ke makotaka da shi da cewar dakarunsa za su janye daga yankunan da suka kama bayan kakkabe mayakan na  Boko Haram, koda sojojin wadannan kasashe sun shirya karbe iko domin tare yankunan ko kuma a’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.