Kamaru

Kotu ta aike da Sojin Kamaru 4 gidan yari na shekaru 10 kan kisan mata

Wani hoton Sojin tare da matan da suka yiwa kisan gillar.
Wani hoton Sojin tare da matan da suka yiwa kisan gillar. Daily Mail

Kotu a Kamaru ta aike da wasu Sojin kasar 4 gidan yari na tsawon shekaru 10 bayan tabbatar da laifinsu na kisan matan nan biyu da ‘ya’yansu kanana, shari'ar da aka dauki tsawon lokaci ana yinta sakamakon yadda kisan ya ja hankalin Duniya.

Talla

Kotun wadda ta yi zamanta a birnin Younde na Kamaru yau Litinin, baya ga hukuncin na shekaru 10 ta kuma karawa Sojin 4 wasu shekaru biyu na daban duk dai kan laifin kisan gillar ga matan biyu da 'ya'yansu.

Bidiyon kisan wanda ya bazu cikin shekarar 2018, ya nuna Sojin na Kamaru 7 na tisa keyar matan dauke da goyon 'ya'yansu bayan sun rufe musu ido da kyalle, inda suka umarcesu su durkusa kafin daga bisani su bude musu wuta tare da kashe su har lahira nan take.

A wancan lokaci dai gwamnatin Kamaru ta tsaya kai da fata kan cewa ba Sojinta ne suka aikata kisan ba, gabanin matsin lambar kasashe da kungiyoyin kare hakkin dan adam da suka bukaci tsananta bincike don tabbatar da adalci kan batun.

Bayan da Kamaru ta aminta da cewa Sojinta ne suka aikata kisan ne Kotu ta fara shari'ar da ta kai ga wanke 3 daga cikinsu yayinda yanzu 4 suka fuskanci hukuncin daurin na shekaru 10.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.