Mali

Tsohon ministan tsaron Mali zai jagoranci gwamnatin hadakar watanni 18

Kanal Assimi Goita, jagoran mulkin Soji a Mali da zai rike mukamin mataimakin shugaban kasa bayan kafa gwamnatin rikon kwaryar watanni 18 a juma'a mai zuwa.
Kanal Assimi Goita, jagoran mulkin Soji a Mali da zai rike mukamin mataimakin shugaban kasa bayan kafa gwamnatin rikon kwaryar watanni 18 a juma'a mai zuwa. MICHELE CATTANI / AFP

Sojin da ke jagorancin Mali sun bayar da sunan tsohon ministan tsaron kasar Bah Ndaw a matsayin sabon shugaban kasa a gwamnatin hadakar da ake shirin kafawa ta watanni 18 gabanin mika mulki ga farar hula.

Talla

Shugabancin Sojin na Mali karkashin Kanal Assimi Goita da ke bayar da sanarwar sunan tsohon ministan tsaron kasar ta wani jawabin kai tsaye a gidan talabijin ya ce shi da kansa zai zamo mataimakin shugaban kasa a gwamnatin hadakar ta tsawon watanni 18 gabanin komawa tsarin demokradiyya kamar yadda aka cimma jituwa.

Tsohon ministan tsaron na Mali Bah Ndaw da ya taba rike mukamin dogarin tsohon shugaban kasar ta Mali Moussa Traore da ya mutu a makon da ya gabata yana da shekaru 83.

Gabanin hambarar da gwamnatin Ibrahim Boubacar keita a watan Agustan da ya agbata ne, Ndaw ke matsayin ministan tsaro, wanda kuma ya samu horo na musamman a tsohuwar tarayyar Soviet baya ga makarantar horar da Soji da Ecole de Guerre a Faransa.

Sanarwar ta nadin Ndaw na zuwa ne bayan dogon taron da kwamitin da aka dorawa alhakin zabar shugaban ya gudanar, haka zalika zaben na zuwa bayan kungiyar ECOWAS ta bai wa sojin wa’adin kwanaki kan su gaggauta nadin farar hula ko kuma su fuskantar karin takunkumai.

Kamar yadda shugaban mulkin Sojin na Mali Assimi Goita ya sanar, a juma’a mai zuwa Bah Ndaw zai sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.